Kwankwasiyya Amana

KWANKWASO KADAI JAM'IYAR APC KE TSORO A DUK FADIN  NIGERIA

Ya Kamata Mutane Su Fuskanci Dalilin Da Yasa Jam'iyar APC Suka Murde Zaben Jihar Kano.
Ba Sunyi Hakanne Saboda Abba Gida Gida Bah

A'a Sunyi Hakanne Domin Karya Kashin Bayan Kwankwaso A Siyasa , Domin Abinda Masana Masu Fashin Baki Akan Sha'anin Siyasa  Suka Binciko Shine Bayan Shugaban Kasa Muhammad Buhari,  Babu Wani Dan Siyasa Da Yakai Madugu Kwankwaso Farin Jini Da Yawan Magoya Baya A Duk Fadin Nigeria

Sanin Kowa Ne Cewa 2023 Ba Buhari Ne Dan Takarar APC Ba Domin Wa'adinsa Ya Kare
Sannan Akwai Yarjejeniya Tsakanin Buhari Da Yarabawa Cewa Sune Zasu Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Yankinsu

Siyasar Kano Tana Da Mutukar Tasiri A Arewacin Nigeria Domin Kuwah Duk Dan Takarar Shugaban Kasar Da Alummar Jihar Kano Suke Goyawa Baya Bincike Ya Tabbatar Da Cewa Shine Wanda Mutanen Arewa Suke Nunawa Goyan Baya Wannan Shine Dalilin A Ake Kiran Kano Da Cibiyar Siyasar Arewa

Idan Kwankwaso Yana Da Gwamna A Jiharsa Topha Xai Samu Dama Wajen Neman Goyon Bayan Gwamnonin Jam'iyar PDP Dasu Mara Masa Baya A Zaben Primary Election Na PDP

Ita Kuma Jam'iyar APC Abinda Bataso Kenan Domin Mutukar Kwankwaso Ya Samu Tikitin Tsayawa Takarar Shugabancin kasa  A Jam'iyar (PDP) Topha Zai Zamo Barazana Babba Ga Yarabawa Da Dan Takararsu Domin Mutanen Arewa Ba Zasu Bar Kwankwaso Su Zabi Bayeraba

Kwankwaso Zai Samu Tikitin Tsayawa Takarane Mutukar Abba Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano, Domin kuwah Idan Kwankwaso Bashi Da Gwamna Topha Zaiyi Wahala Sosae Ya Samu Tikitin Takarar Shugabancin Kasa PDP,

Wanda Hakan Shine Bukatar Jam'iyar APC Domin Sun Yarda Kowa Ya Samu Tikitin Amma Banda Kwankwaso

A Matsayinka Na Dan Kishin Arewa Wanne Fata Kake Yiwa Kwankwaso A Shekarar 2023

IBRAHIM SADI BACHIRAWA
02/05/2019

Comments

Popular posts from this blog

Jamb update

JAMB

Ramadan calendar in sokoto